Hukumar FCTA Ta Fatattaki Mabarata 607 Daga Titunan Abuja
[ad_1]
Hukumar babban birnin tarayya (FCT), ta kori mabarata 607 da masu taɓin hankali a titunan Abuja daga watan Yulin 2025 zuwa wnnan lokaci da muke ciki.
Ukachi Adebayo, shugabar zartarwa ta sakatariyar ci gaban zamantakewa na FCT, SDS, ita ce ta bayyana hakan, a wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Abuja, ranar Litinin.
- FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m
- Ma’aikatan FCT Sun Fara Yajin Aiki, Sun Rufe Ofisoshin FCTA Da FCDA
Madam Adebayo ta ce, rundunar ‘Operation Sweep Abuja’ ce ta gudanar da atisayen, domin fatattakar duk wasu masu aikata laifuka a cikin birnin.
Ta ƙara da cewa, daga cikin mutane 607 da aka kwashe, 583 mabarata ne; yayin da 23 kuma masu tavin hankali ne.
Har ila yau, ta ci gaba da cewa, mabarata da masu tavin hankalin, an yi musu nasiha tare da bayyana sunayensu da kuma mayar da su jihohinsu daban-daban ta hanyar yin haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi ta ofisoshin hulɗa da su.
“Abin da muke yi lokacin da muka kama mabaratan da masu tavin hankali shi ne, mun ja hankalinsu tare kuma da yi musu nasiha.
“Bayan haka, muna kai su ofisoshin hulɗa da su daban-daban, don mayar da su jihohinsu; inda ake sa ran za a ja musu kunne,” in ji ta.
Da take lura da cewa, mabaratan da masu tavin hankali, suna komawa kan tituna bayan an kwashe su, Madam Adebayo ta ce, ana ci gaba da gudanar da aikin bincike, sannan kuma za a ci gaba da kwashe su daga kafatanin titunan Abuja.
Ta ce: “Yayin da ake fitar da su; wasu kuma suna sake dawowa.
“Wasu daga cikinsu, rashin tsaro ne ya sa su a jiharsu suka gudo zuwa Abuja, domin fakewa; amma za mu ci gaba da kama su tare da mayar da su garuruwansu”.
[ad_2]
Source link