Sanata Barau Ya Ziyarci Sansanonin Sojoji 4, Ya Buƙaci Murƙushe Ƴan Ta’adda

[ad_1]

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ziyarci sansanonin sojoji a ƙananan hukumomin Gwarzo, Shanono da Tsanyawa na Yankin Kano ta Arewa, domin ƙarfafawa gwuiwar dakarun tsaro da aka tura yankin bayan hare-haren ƴan bindiga daga jihohin makwabta. Ziyarar ta biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na tura sojoji, da ƴansanda da jami’an NSCDC domin daƙile barazanar tsaro a yankin.

A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, Sanata Barau ya isa Kano da misalin karfe 7 na safe, inda ya fara ziyarar ne a Lakwaya, ƙaramar hukumar Gwarzo. A nan ne ya duba jerin dakarun tsaro tare da Kwamandan Barikin Rundunar Sojin Ƙasa ta 3 Brigade, Laftanar Kanal I. Ekoh, da sauran manyan jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan JTF na Gwarzo, Laftanar Abdullahi Sadiq.

  • Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano
  • Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

Da yake jawabi ga dakarun, Sanata Barau ya yabawa jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai godewa Shugaban Ƙasa bisa gaggauta ɗaukar matakin tura su yankin. Ya buƙaci sojojin da su ci gaba da matsa lamba kan ƴan bindiga, su bi su ko’ina suke tare da korarsu daga yankunan Kano gaba ɗaya domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Daga nan, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya ci gaba da ziyarar sansanonin sojoji a Tsaure da Faruruwa na ƙaramar hukumar Shanono, da kuma sansanin Tsanyawa, inda ya ƙarfafa musu gwuiwa. Ya kuma buƙaci al’ummomi da su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai da bayanai domin tabbatar da nasarar yaƙi da ta’addanci.

A wata ganawa da shugabannin al’umma a Faruruwa, dattijo Alhaji Yahaya Bagobiri ya gode wa Sanata Barau bisa ƙoƙarinsa wajen ganin an tura jami’an tsaro da kuma aiwatar da wasu ayyukan raya ƙasa. Sanatan ya tabbatar wa jama’a cewa za a gina dam a yankin nan ba da jimawa ba, yana mai addu’ar Allah Ya kare yankin daga sake faruwar irin waɗannan hare-hare.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *