AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Algeria A Wasan Kwata Fainal
[ad_1]
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya zata hadu da takwararta ta kasar Algeria a wasan zagayen Kwata Fainal na gasar kasashen nahiyar Afirika da ake cigaba da bugawa a Morocco, Nijeriya ta karshe zagayen Kwata Fainal bayan lallasa kasar Mozambique a wasan zagayen yan 16 a ranar Litinin.
Hakazalika Algeria ta doke Dimokuradiyyar Congo a wasan zagayen 16 da ci 1-0 bayan karin mintuna 30 da alkalin wasa yayi a wasan, kasashen biyu zasu hadu a ranar Asabar 10 ga watan Janairu domin sanin kasar da zata kai matakin Semi Fainal.
Nijeriya ta samu nasara a dukkan wasanni 4 da ta buga a gasar ta bana, ta jefa kwallaye 12 yayinda aka zura mata kwallo 4 kacal a raga, a bangaren Algeria kuma The Desert Foxes kamar yadda ake kiransu sun zura kwallaye 8 a raga inda aka jefa masu kwallo 1 kacal a ragarsu.
[ad_2]
Source link