Tinubu ya naɗa mace ta farko shugabar Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya

[ad_1]



Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dakta Olugbemisola Titilayo Odusote a matsayin sabuwar Darakta-Janar ta Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law School).

Wannan naɗi ya sanya Dakta Odusote ta zama mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun bayan kafa ta a shekarar 1962.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce naɗin zai fara aiki daga ranar 10 ga Janairu, 2026, na tsawon shekara huɗu.

Dakta Odusote, mai shekaru 54, a halin yanzu ita ce mataimakiyar shugabar reshen Makarantar Horar da Lauyoyi da ke Jihar Legas.

Sanarwar ta ƙara da cewa za ta gaji Farfesa Isa Hayatu Chiroma, shugaban makarantar mai barin gado, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 9 ga Janairu, 2026, bayan shafe shekara takwas yana jagorancin makarantar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *