2027: Babu Wani Ɗan Takara Da Zai Haƙurar Ma Wani Takararsa A ADC – Atiku

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 a jam’iyyar ADC da zai hakurar ma wani da takarar sa, duk ‘yan takara, za a ba su ‘yancin yin takara.

Atiku, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Talata, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da farfagandar da Jam’iyyar APC ke yi na sanya rauni a zukatan ‘yan jam’iyyar.

Atiku, ya yi tsokaci ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa yana fuskantar matsin lamba kan ya hakura da takararsa ya bar wa ɗan takara daga Kudu a matsayin wanda zai ja ragamar jam’iyyar ADC a zaɓen da ke tafe domin kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya ƙara da cewa, idan akwai wanda ya kamata ya sauka, to Shugaba Bola Tinubu ne, wanda shugabancinsa ya zama babban kalubale ga Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *