Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru

[ad_1]



Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru.

“Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya.

Binciken bayan harin ya nuna cewa an binne gawarwaki fiye da 20, ciki har da sassan jikin da suka tarwatse, an kuma kwato makamai daga hannun ’yan ta’addan.

Kakakin rundunar sojin sama, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya tabbatar da harin, yana mai cewa fiye da ’yan ta’adda 35 ne aka kashe a hare-haren.

Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *