Satar ayaba ya yi sanadin mutuwar mutum 2 a Kuros Riba

[ad_1]



Wasu mutum biyu sun yi mutuwar ragas a dalilin rikicin da ya ɓarke bayan zargin satar ayabar soyawa (plantain) a yankin ƙaramar hukumar Odukpani da ke Jihar Kuros Riba.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Akpap-Okoyong, inda wani manomi mai suna Effiong ya yi arangama da Edet, wanda ya yi zargi cewa ya sato ayabar ce a gonarsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba, ASP Sunday Eyo Eitokpah, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici da tayar da hankali.

Ya ce, “lamarin ya samo asali ne bayan da wani ya sanar da Effiong cewa ya ga Edet da sanyin safiyar Litinin yana fitowa daga wata gona ɗauke da curi-curi na ayabar filanten a kafaɗarsa, yana hanzarin komawa gida.”

A cewar kakakin ’yan sandan, wannan tsegumi da aka kai wa Effiong ne ya janyo aka yi arangama tsakanin mutanen biyu, lamarin da daga bisani ya rikiɗe zuwa faɗa mai muni.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jami’an tsaro cewa Effiong da Edet sun shiga bai wa hammata iska ne, inda kowanne daga cikinsu da ke riƙe da adda, suka riƙa sara wa juna.

Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko dai Effiong ya tunkari Edet a kan hanya bayan ya gano ayabarsa ta ɓace, yana zarginsa da satar amfanin gonar inda ya nemi ya mayar masa da ita.

Sai dai rikicin ya ƙazance, inda suka fara sara wa juna adda ba tare da wani ya samu damar raba su ba.

’Yan sanda sun ce sun fara cikakken bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abin da ya faru tare da ɗaukar matakan da suka dace a kai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *