Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun daƙile harin jirage mara matuƙa a Borno

[ad_1]



Dakarun haɗin gwiwar rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun daƙile hare-haren jirage mara matuƙa tare da lalata sansanonin Boko Haram da ISWAP a yankin Timbuktu Triangle na Jihar Borno.

A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce an kashe ’yan ta’adda da dama yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Ya ce dakarun sun ƙwato makamai, harsasai da kayan aiki na dabarun yaƙi a yayin samamen da aka gudanar bisa bayanan sirri a Chilaria, Garin Faruk da Abirma.

“Aikin ya samu goyon bayan jiragen yaƙi da suka samar da bayanan leƙen asiri, sa ido da kuma bincike a kai a kai.

“Wannan haɗin gwiwar sama da ƙasa ya taimaka wajen bin diddigin motsin ’yan ta’adda a zahiri, ya hana su samun ƙarin goyon baya, ko damar kai hare-haren ƙasa,” in ji shi.

Kanar Uba ya bayyana cewa kayan da aka ƙwato sun haɗa da rediyon Baofeng, mazuban harsasan AK-47, harsasan 7.62mm da 12.7mm, tutocin Boko Haram/ISWAP, kayan magani, injinan niƙa masu amfani da dizel, buhunan hatsi, motar ɗaukar kaya, wuraren ajiya na ƙarƙashin ƙasa da kuma man fetur da man inji.

Ya ce dakarun sun gamu da hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai da rana da kuma yamma, amma sun ci gaba da matsa lamba har suka tilasta ’yan ta’addan janyewa.

Kanar Uba ya ƙara da cewa rundunar ta ƙuduri aniyar kawar da barazanar ta’addanci, kare rayukan jama’a da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *