Mataimakin Ministan Wajen Sin: Nuna Karfin Tuwo Ba Abun Da Zai Haifar Sai Koma Baya
[ad_1]
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong, ya ce Sin ta gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI, a watan Satumban shekarar da ta gabata, wadda ta samu goyon bayan kasashe sama da 150. Kuma a gabar da duniya ke fuskantar karin kalubale, Sin na aiki tukuru tare da dukkanin sassa, wajen ingiza aiwatar da shawarar ta GGI tare da zurfafa ma’anarta.
Sun, wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi a daidata alakar dake akwai tsakanin kasashe daban daban ta amfani da dokokin kasa da kasa, maimakon barin wasu kasashe tsiraru suna cin zalin wasu ba. Ya ce a duniyar yau, matakin amfani da karfin tuwo ba zai haifar da ‘da mai ido ba. Kuma kamata ya yi kasashe musamman masu karfin fada-a-ji, su wuce gaba wajen nacewa biyayya ga tsarin doka da ka’ijojin kasa da kasa.
Daga nan sai Sun ya bayyana cewa, ya zama wajibi a yayata ruhin dokokin kasa da kasa, da kyautata iko, da ingancin ayyukan hukumomin kasa da kasa, kana a nuna adawa ga salon nuna karfin tuwo, wanda ke baiwa mai karfi damar zaluntar mai rauni, da nuna turjiya ga salon babakere, irin na amfani da karfin soji domin yiwa wasu sassa matsin lamba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link