Ka Manta Da Komai, Ka Bar Abba Ya Yi Wa Kano Aiki — Matar Ganduje Ga Kwankwaso
[ad_1]
Matar Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, ta buƙaci tsohon gwamnan jihar kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da ya manta da saɓanin siyasa ya kuma bar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da mulki domin amfanin al’ummar Kano.
Ta yi wannan kiran ne yayin shirin tallafi da ƙaramar ministar babban birnin tarayya, Mariya Bunkure, ta shirya, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai.
- Ayyukan ‘Yan Daba A Kano: Kira Ga Shugabanni Da Malamai Da Masu Fada A Ji
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbo Na Gwaji Da Za A Iya Sake Amfani Da Shi
“Abba Kabir Yusuf ya yi aiki ƙarƙashin Kwankwaso na tsawon shekaru, don haka ina roƙonsa da ya ajiye saɓanin da ke tsakaninsu ya bar gwamnan ya yi aiki domin ci gaban Kano,” in ji ta.
Farfesar ta kuma buƙaci ‘yan jam’iyyar APC da su mara wa gwamnan baya, biyo bayan komawarsa jam’iyyar, domin tabbatar da ci gaban jihar.
“Yanzu da gwamnan Jihar Kano ya dawo APC, ya kamata dukkanin mambobin jam’iyyar, tsofaffi da sababbi su haɗa kai domin ciyar da Kano gaba,” in ji ta.
[ad_2]
Source link