Ƙofor APC A Buɗe Take Ga Kwankwaso — Yilwatda

[ad_1]

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki a shirye take ta karɓi tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, idan ya yanke shawarar shiga APC.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Trust TV a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, biyo bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya jawo wasu ƴan Majalisar Dokokin Jiha da na Majalisar Wakilai su bi sahunsa.

  • Yadda Buƙatun Kwankwaso Suka Tarwatsa Yiwuwar Haɗin Gwuiwa Da APC
  • Jami’ar MAAUN Da Kwalejin Seneca ta Canada Sun Yi Haɗin Gwiwa Domin Samar Da Damarmaki Ga Ɗalibai A Duniya

Ƙofofinmu a buɗe suke ga Kwankwaso ya shigo APC. Idan ya zo, maraba zai yi masa,” in ji Yilwatda. “Amma a halin yanzu ba mu shiga tattaunawa da shi ba.”

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa APC na ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar a Jihar Kano, wacce ake ganin tana daga cikin jihohin da za su taka muhimmiyar rawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban jam’iyyar ya kuma kare yawan tafiye-tafiyen ƙasashen waje da Shugaba Bola Tinubu ke yi, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa matsayin Nijeriya a idon duniya da jawo zuba hannun jari. Ya jaddada cewa tafiye-tafiyen na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa haɗin gwuiwar tsaro tsakanin Nijeriya da ƙasashen waje.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *