An ƙaddamar da riga-kafin karnuka 2,500 a Gombe
[ad_1]
Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya ta ƙaddamar da yunƙurin ƙasa baki ɗaya na yin riga-kafi kyauta ga karnuka da maguna domin yaƙar cutar haukan kare inda Jihar Gombe ke shirin yin riga-kafi ga karnuka 2,500 a matakin farko.
Da take jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, Babbar Sakatariya na Ma’aikatar, Dokta Chinyere Akujobi wadda Mataimakiyar Darakta, Dokta Salome Bawa ta wakilta ta bayyana cewa cutar haukan kare na ci gaba da hallaka dubban mutane a duk shekara a faɗin duniya, musamman a nahiyoyin Afirka da Asiya.
Ta ce, mafi yawan waɗanda ke mutuwa sakamakon cutar yara ne ’yan ƙasa da shekara 15, wanda hakan ke nuna cewa haukan kare ba wai matsalar lafiya kaɗai bace, matsala ce ta zamantakewa da ke shafar iyalai da al’umma baki ɗaya.
Dokta Bawa ta bayyana cewa, haukan kare cuta ce da za a iya kauce mata gaba ɗaya ta hanyar yin riga-kafi ga karnuka da maguna waɗanda su ne manyan hanyoyin yaɗa cutar ga mutane.
Ta ce, daga cikin allurai 26,000 na riga-kafin haukan kare da aka tanada a wannan matakin na farko, Jihar Gombe ta samu allurai 2,500, waɗanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, za su taimaka wajen rage yaɗuwar cutar a jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Noma da Kiwo na Jihar Gombe, Mista Barnabas Malle, ya bayyana cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na da cikakken ƙudiri na kare lafiyar dabbobi da namun gida daga cututtuka masu cutarwa.
Ya tunatar da cewa jihar ta taɓa yin riga-kafin shanu domin kare su daga cutar huhu (anthrax) a bara, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da Ma’aikatar Tarayya domin faɗaɗa shirye-shiryen kiwon lafiyan dabbobi.
Farfesa Grace Sabo Nok Kia daga Kungiyar War Against Rabies Foundation ta yaba da wannan shiri, amma ta buƙaci a samar da ƙarin allurai domin tabbatar da cewa kowanne kare da mage a jihar su samu riga-kafi.
Ta buƙaci likitocin dabbobi da su tabbatar da gaskiya da adalci wajen rarrabawa da yin amfani da riga-kafin yadda ya dace.
Haka kuma ta roƙi masu karnuka da su kai dabbobinsu cibiyoyin rigakafi, tana mai cewa kawar da cutar haukan kare na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link