Tinubu ya ba wa Abba tabbaci
[ad_1]
Ana sa ran a kowane lokaci daga yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano zai iya sanar da sauya sheƙarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Alamun hakan sun bayyana ne bayan ganawar sirrin da Gwamna Abba ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Litinin.
Majiyoyi masu kusanci sun bayyana cewa ganawar Gwamna Abba da Tinubu ta Yammacin ranar Litinin zuwa cikin dare ta shawo kan wasu batutuwa da a baya suka kawo tsako ga sauyin sheƙarsa daga NNPP zuwa APC.
Wannan ya ba da damar ci gaba da shirin dawowarsa APC a hukumance wanda ake da ran sanarwar a kowane lokaci daga yanzu.
Ganawar shugabannin wadda ta gudana bayan dawowar Tinubu daga ƙasashen waje, ta zo ne bayan an jima ana ce-ce-ku-ce game da sauya sheƙar Abba da kuma tsamin dangantaka tsakaninsa da uban gidansa na siyasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran NNPP.
Majiyoyinmu sun ce Gwamna Abba ya fara raba ɗaya biyu kan sauya sheƙar ne a cikin ’yan makonnin nan game da makomarsa a APC, musamman tabbacin samun tazarcensa a zaɓen 2027 da kuma makomar tsarinsa na siyasa da makomar magoya bayansa idan sun koma APC.
Sai dai sun tabbatar da cewa gwamnan ya samu tabbacin Tinubu kan waɗannan buƙatu a yayin tattaunawar wadda aka kammala a cikin dare ranar Litinin.
“Zai sanar sauya sheƙar tasa a hukumance ranar Talata ko Laraba, saboda an riga an magance duk batutuwan. Shugaban Ƙasa yana buƙatar gwamnan a APC kuma shi ma gwamnan yana son kasancewa tare da shugaban kasa,” in ji wata majiya da ke da kusanci da lamarin.
Tun da aka fara wannan dambarwar, har yanzu Gwamna bai ce uffan ba kan lamarin.
Ko bayan fitowarsa daga tattaunawat a Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 7 na dare ranar Litinin, ya ki yi wa ’yan jarida.
Duk da cewa sun tambaye shi, kawai cewa ya yi, “zan dawo,” ba tare da wani ƙarin bayani ba.
Yunkurin sauya sheƙar Abba ya ƙara ɗaukar hankali
A karshen shekarar da ta gabata aka fara raɗe-raɗin sauya sheƙar Gwamna Abba bayan wasu alamu na siyasa da suka nuna yana sake duba dangantakarsa da Gwamnatin Tarayya ta APC.
Ko da yake gwamnan bai taba bayyana a fili kan batun ba, muƙarrabansa da abokan siyasarsa sun daɗe suna mu’amala da manyan jagororin APC a Kano da Abuja, abin da ya ƙara ƙarfafa bautin sauyin sheƙar.
Sai dai rahotanni a makon jiya sun nuna cewa shirin nasa ya samu tangarɗa, bayan shugabannin APC sun nuna taka-tsantsarsu wajen bayar da cikakken tabbaci, musamman kan tikitin tazarcensa kai tsaye a 2027.
Wannan, a cewar majiyoyi, ya sa shi jinkirtawa, Kodayake wasu magoya bayansa a matakin ƙananan hukumomi da gundumomi sun riga sun fara komawa APC.
Sai dai ganawarsa da Tinubu a ranar Litinin ta sake ba wa shirin nasa ƙarfi.
Majiyoyinmu sun ce shugaban ƙasa ya tabbatar masa da muhimmancinsa a lissafin siyasar APC, musamman a Kano da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya, inda jam’iyyar ta yi rauni a zaben 2023.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link