Zargin Sace Masu Ibada Fiye Da 100 A Kaduna Ba Gaskiya Ba Ne – ‘Yansanda

[ad_1]

Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna, Muhammad Rabiu, ya bayyana rahoton sace masu ibada sama da 100 a Kurmin Wali, a karamar hukumar Kajuru, a matsayin ƙarya da marasa kishin ƙasa ke yaɗawa waɗanda ke son haifar da rikici a Jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron Majalisar Tsaron Kasa a gidan Gwamnati na Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna a ranar Litinin, Kwamishinan ya kalubalanci duk wanda yake da Cikakken bayani ko jerin sunayen waɗanda aka sace da ya kawo.

  • Mataimakin Ministan Wajen Sin: Nuna Karfin Tuwo Ba Abun Da Zai Haifar Sai Koma Baya
  • Jerin Kyaututtukan Da Aka Bayar Bayan Kammala Gasar AFCON 2025

Kwamishinan ya gargaɗi masu yaɗa jita-jita da su daina kokarin kawo cikas ga zaman lafiyan da Jihar Kaduna ke da shi, yana mai barazanar cewa za a hukunta irin waɗannan miyagun mutane masu yaɗa labaran ƙarya.

Shugaban karamar kumar Kajuru, Dauda Madaki, ya ce lokacin da ya ji labarin harin, ya tattara ‘yansanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin Kurmin Wali, amma ya gano cewa babu wannan harin.

“Mun ziyarci cocin da ake zargin lamarin sace mutanen ya faru. Babu wata shaida game da harin.” Na tambayi hakimin ƙauyen, Mai Dan Zariya, sai ya ce babu wani hari makamancin haka.

A martanin da ya mayar, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Sule Shuaibu (SAN), ya ce shugaban CAN da sauran shugabannin addini duk sun ziyarci yankin don tabbatar da rahoton amma duk an gano babu makamancin irin wannan harin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *