An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa

[ad_1]



Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa.

Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya shigo daga jihar Ribas ne musamman domin amfani da taron siyasar da aka shirya wajen yin sata.

Ya ce jami’ansu sun kama shi ne bayan sun lura da motsinsa da ya sa suka zarge shi. Bayan bincike, sai suka gano wayoyi 17, kudi N91,000, da kuma katunan ATM da dama a cikin jaka da yake dauke da ita.

Alagba ya kara da cewa, Francis ya shaida musu cewa yana aiki tare da wasu abokan laifi da suka tsere yayin kamun.

Ya kuma bayyana cewa kafin a kama shi, sun riga sun kwashe sama da N400,000, sannan daya daga cikin wadanda suka gudu yana da karin wayoyi da sauran kayayyakin da suka sace.

Shugaban sa-kai din ya gargadi masu aikata laifuka da su guji shiga Bayelsa, yana mai cewa jami’ansa sun samu horo na musamman kan tattara bayanan sirri, lura da halayen jama’a da kuma tsaron taruka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *