Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana dalilin da ya sa sauran sanatoci ba su mara mata goyon baya ba lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida a Majalisar Dattawa.
Yayin buɗe sabuwar kasuwa a garin Okene, Jihar Kogi, Natasha ta ce yawancin sanatoci sun ji tsoron zaluncin siyasa idan suka goyo maga baya a bainar jama’a.
Ta bayyana cewa wasu daga cikin abokan aikinta sun kira ta da kansu sun kuma tausaya mata tare da goyon bayanta, amma sun guji yin hakan a fili saboda tsoron hukunci ko tsangwama.
“Idan jami’in gwamnati ya shiga matsala, mutane kan rabu da shi,” in ji ta.
“Da dama daga cikin sanatoci sun goyi bayana a sirrance, sun kira ni, wasu ma sun zo sun ganni amma ba su iya nuna hakan a bainar jama’a ba. Ban ji haushi ba.”
Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati.
An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba bayan kammala wa’adin dakatarwar.