Gwamnatin Sojin Burkina Faso Ta Rushe Duk Jam’iyyun Siyasar Ƙasar
[ad_1]
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta rushe dukkan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyinsu tare da soke dokokin da ke tafiyar da ayyukansu, a wani mataki mai faɗi da ke kawo ƙarshen siyasar jam’iyyu a hukumance a ƙasar. An sanar da wannan mataki ne ta hannun sashin yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa bayan zaman majalisar ministoci da shugaban mulkin soji wanda Kyaftin Ibrahim Traoré ya jagoranta.
Ministan Harkokin Gudanar da Yankuna, Émile Zerbo, ya ce wannan mataki na daga cikin abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin “sake gina ƙasa.” A cewar sanarwar, gwamnati ta shaida cewa yawaitar jam’iyyun siyasa ya taimaka wajen rarraba al’umma da raunana haɗin kan jama’a a ƙasar.
- Bayan Tsare Jami’an Sojin Nijeriya A Burkina Faso, Nijar Ta Sanya Tsauraran Bincike Kan Kayayyakin Nijeriya
- Wazirin Ningi Ya Yi Murabus Bisa Zargin Shigar Da Siyasa Cikin Harƙoƙin Masarautar
“Matakin na da nufin kare haɗin kan ƙasa, ƙarfafa daidaiton ayyukan gwamnati, da kuma buɗe hanya don sake fasalin tsarin tafiyar da siyasa,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasar. Bisa ga dokar da majalisar ministoci ta amince da ita, duk kadarorin jam’iyyun siyasar da aka rushe za a miƙa su ga gwamnatin ƙasa.
Zerbo ya ƙara da cewa za a gabatar da ƙudirin doka don tabbatar da wannan mataki a gaban Majalisar Dokokin Riƙo a cikin kwanaki masu zuwa. Kafin yin juyin mulkin, Burkina Faso na da sama da jam’iyyun siyasa 100 da aka yi wa rajista, inda 15 daga cikinsu ke da wakilci a majalisa bayan zaɓen 2020.
A wani ɓangare na zaman majalisar ministocin, gwamnati ta kuma amince da sabon tsarin bunƙasa ƙasa da ake kira “Shirin Dogaro da Kai (Reliance Plan),” wata taswira ta shekaru biyar daga 2026 zuwa 2030 da kimarsa ta kai FCFA tiriliyan 36 (kimanin dala biliyan 65), domin farfaɗo da tattalin arziƙi da tsarin mulki a ƙasar.
[ad_2]
Source link