Darajar Tambarin Kamfanonin Kimiyya Da Fasaha Na Kasar Sin Ta Samu Karuwa

[ad_1]

Bisa rahoton da wani babban kamfanin binciken tambarin kamfanoni ya gabatar a jiya Alhamis, darajar tambarin kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar Sin ta samu karuwa, wadda ta zarce ta kasar Japan a karo na farko, tare da zama matsayin farko a duniya a wannan fanni, hakan ya tabbatar da matsayin Sin mai ci gaban kimiyya da fasaha a duniya.

Bisa rahoton jerin sunayen tambarin manyan kamfanonin kimiyya da fasaha 100 na shekarar 2026 da aka gabatar, an ce, darajar tambarin manyan kamfanonin 100 ta kai dala triliyan 3.7, wadda ta karu da kashi 15 cikin dari bisa na bara.

Kamfanonin Sin guda 25 suna cikin jerin sunayen, inda Sin ta kasance a matsayi na biyu a duniya a wannan fanni, darajar kamfanonin ta kai dala biliyan 465. Kana bisa wannan rahoto, kamfanonin Sin guda 11 sun shiga jerin sunayen kamfanoni 50 dake kan gaba a duniya a wannan fanni.

Rahoton ya yi nuni da cewa, darajar tambarin kamfanonin Sin a wannan fanni ta samu karuwa cikin sauri, wadda ta karu da kashi 27.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara, inda kasar Sin ta zama a kan gaba cikin manyan kasashe masu mallakar kamfanonin kimiyya da fasaha dake cikin jerin sunayen. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *