Fitattun Jaruman Kannywood da suka riga mu gidan-gaskiya a 2025
[ad_1]
Fitattun Jaruman Kannywood da suka riga mu gidan-gaskiya a 2025
Masana’antar Kannywood a wannan shekara ta 2025 ta yi rashin wasu fitattau daga ‘ya’yanta waxanda suka kasance jiga-jigai da dattawa da kuma matasa.
Kamar yadda Jaridar Aminiya ta kalato maku daga Sashen Hausa na BBC Landan da sauran kafafen yaxa labarai na intanet, jaruman da suka rasu a wannan shekarar sun haxa da:
Baba Karkuzu
Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Karkuzu fitaccen jarumi ne na finafinan Hausa da ya daxe yana nishaxantar da al’umma.
Baba Karkuzu ya fara yin fice ne a fim xin da ya fito mai suna “Karkuzu na Bodara,” wanda aka yi a tsakankanin 1980.
Suna cikin jaruman da suka fara assasa fina-)finan Hausa a Arewacin Nijeriya kafin matasan jaruman su taso.
Ya rasu ne a ranar 25 ga watan Maris na wannan shekarar ta 2025 yana da shekara 94.
Ya rasu ne a birnin Jos na jihar Filato bayan fama da jinya na tsawon lokaci, inda har makancewa ya yi.
Nata’ala dare
Malam Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala Mai Sittin Goma ya rasu a ranar Lahadi 2 ga watan Nuwamba. An haife shi ne a Rijiyar Damuwa da ke Qaramar Hukumar Potiskum ta Jihar yobe. Ya fara karatun Allo a Yola ta Jihar Adamawa a 1979.
Ya rasu ya bar mata 3 da yara da dama, sannan ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya sha. An yi jana’izarsa a ranar Litinin 3 ga watan Nuwamba a Jihar Yobe.
Umar Maikuxi
Jarumi Umar Maikudi da ake wa laqabi da Cashman ya rasu a garin Zariya da ke Jihar Kaduna a cikin watan Mayun wannan shekarar ta 2025.
Marigayin ya fito a shirin ‘Labarina’ mai dogon zango, sannan ya kasance shugaban Qungiyar Masu Shirya shiryaFinafinai ta Nijeriya. Ya rasu ya bar mata da yara.
Dream Hasin
Fitaccen jarumin finafinan Kannywood, Muhammad Shuaibu, wanda aka fi sani da Baba Hasin ya rasu a ranar Asabar 27 ga watan Afrilun wannan shekarar. Jarumin wanda yake fitowa a matsayin dattijo sananne ne a cikin finafinai masu dogon zango.
Jarumin ya rasu ne yana da shekara 68 a duniya bayan shafe tsawon lokaci yana jinya a Asibitin Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano. Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 17.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link