An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa

[ad_1]


Wata kotun ta musamman a kasar Bangladesh ta yanke wa tsohuwar Firaminista, Sheikh Hasina, hukuncin kisa a ranar Litinin bisa zargin aikata laifukan cin zarafin bil’adama da suka shafi zanga-zangar dalibai ta bara, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane kuma ta kawo ƙarshen mulkinta na tsawon shekaru 15.

Kotun ta kuma yanke wa tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Asaduzzaman Khan, hukuncin kisa, yayin da tsohon Sufeton ’Yansanda kuma ya samu hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar bayan ya amsa laifi.

Hukuncin, wanda aka karanta a babban birnin Dhaka, an watsa shi kai tsaye ta talabijin. Kafin hukuncin, gwamnatin rikon kwarya ta ƙara tsaurara tsaro a fadin ƙasar ta hanyar tura jami’an iyaka da yansanda musamman a Dhaka da sauran yankuna. Jam’iyyar Awami League ta Hasina ta sanar da rufe ƙasa baki daya a matsayin martani ga hukuncin.

Hasina da Khan, wadanda ke gudun hijira a Indiya, an gurfanar da su ne ba tare da kasancewarsu a kotu ba. Su da jam’iyyarsu sun yi watsi da kotun, suna kiran ta “kotun bogi,” tare da sukar lauyan gwamnati da aka nada musu. Zarge-zargen sun samo asali ne daga tarzomar dalibai ta Yuli zuwa Agusta 2024 wacce ta yi sanadin mutuwar mutane da dama. Rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a Fabrairu ya kiyasta mutanen da suka mutu zuwa 1,400, yayin da wani jami’in kiwon lafiya na gwamnati ya ce sun zarce 800, inda kusan 14,000 suka ji rauni.

A makon da ya gabata, kotun ta tabbatar da ranar Litinin domin yanke hukunci bayan sake barkewar tashin hankali da suka haɗa da fashewar ƙananan bama-bamai da kone-kone da suka katse harkokin makarantu da sufuri bayan jam’iyyar Awami League ta kira rufe ƙasa. Kafin yanke hukuncin, jam’iyyar ta sake nanata kiran rufe ƙasa, inda Hasina ta yi kira ga magoya bayanta ta cikin saƙon murya da kada su ji tsoro game da sakamakon.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *