Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Kasar Koriya Ta Kudu

[ad_1]

Da maraicen yau Litinin 5 ga wata, a Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gudanar da shawarwari tare da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu, Lee Jae-myung, wanda a yanzu haka ke ziyarar aiki kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce, kasar Sin ta yi fatan kokari tare da Koriya ta Kudu, don ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu gaba kuma ta hanyar da ta dace, da kara samar da alfanu ga al’ummun kasashen biyu, da taimaka wa ayyukan wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba a wannan shiyya da ma duniya baki daya. Ya kara da cewa, a matsayinsu na kasashen da suka amfana daga dunkulewar tattalin arzikin duniya, ya dace Sin da Koriya ta Kudu su hada kai don kin yarda da ra’ayin kariyar ciniki, da aiwatar da ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori, tare kuma da bayar da gudummawa ga kara cudanyar mabambantan sassa a duniya, da inganta dunkule tattalin arzikin duniya baki daya.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun shaida yadda aka rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin-gwiwa guda 15 da suka shafi kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da muhallin halittu, da sufuri, da tattalin arziki da kasuwanci da sauransu. (Murtala Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *