Wang Yi Ya Halarci Taron Manyan Jami’ai Karo Na 61 Na Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD
[ad_1]
A yau Litinin, mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron manyan jami’ai karo na 61 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ta kafar bidiyo, tare da ba da jawabi.
A cikin jawabinsa Wang Yi ya bayyana cewa, shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta nuna basirar kasar Sin wajen jagorantar tsarin kare hakkin dan Adam na duniya, wadda kuma ta samu goyon baya daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 150.
Wang Yi ya kara da cewa, kasarsa na son yin aiki tare da kasashe daban daban, wajen amfani da damar tabbatar da shawarar inganta jagorancin duniya wajen kyautata harkokin kare hakkin dan Adam na duniya, da ma ciyar da sha’anin gaba yadda ya kamata.
[ad_2]
Source link