APC Ta Rantsar da Kwamitin Gudanarwar Cibiyar Ci Gaban Siyasa (TPI)

[ad_1]

Jam’iyyar APC ta rantsar da kwamitin gudanarwar Cibiyar Ci Gaban Siyasa (The Progressive Institute (TPI), cibiyar bincike da tunani ta jam’iyyar mai mulki. Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, shi ne shugaban kwamitin, yayin da Sakataren Jam’iyya na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, da wasu manyan jiga-jigai ke matsayin mambobi. Darakta-Janar na cibiyar, Lanre Adebayo, shi ne sakatare.

Da yake ƙaddamar da kwamitin, Yilwatda ya ce matakin wani gagarumin ci gaba ne wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyar da kuma siyasar Nijeriya baki ɗaya. Ya bayyana cewa an kafa cibiyar ne bisa shawarar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, domin zurfafa fahimtar aƙida, inganta bincike da kuma ƙarfafa siyasar da ta dogara da manufofi.

  • Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
  • Zaɓen Mazaɓu Na APC A Sakkwato Alama Ce Ta Haɗin Kai

A cewarsa, TPI za ta mayar da hankali kan gyaran tsarin mulki, da horas da shugabanni, da gina ƙwarewa da kuma tsara manufofi bisa hujjoji domin inganta dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa. Ya ƙara da cewa an yi rajistar cibiyar a Hukumar CAC kuma ta samu amincewa daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da NBTE, domin tabbatar da sahihanci da ɗorewarta.

Yilwatda ya jaddada cewa kwamitin gudanarwa shi ne matakin yanke hukunci mafi girma a cibiyar, yana mai cewa APC za ta tabbatar da cikakken goyon baya ga TPI domin ta zama cibiyar siyasa mai ƙima a duniya. Shi ma Darakta-Janar, Adebayo, ya ce cibiyar ta fara aiwatar da shirye-shiryen horaswa a jihohi daban-daban tare da haɗin gwuiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da Tarayyar Turai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *