Ashe Gwamnatin Najeriya ta biya Boko Haram kuɗin fansa kafin sako ɗaliban Neja?
[ad_1]
Wasu majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta biya ƙungiyar ta’adda ta Boko Haram kuɗin fansa masu yawan gaske da aka ƙiyasta sun kai miliyoyin daloli gabanin sakin yara da ma’aikata kusan 230 da aka sace daga wata makarantar sakandire a Jihar Neja a watan Nuwamba da ya gabata.
Majiyoyin sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa a cikin yarjejeniyar, an kuma saki kwamandoji biyu na Boko Haram, lamarin da ya saɓa wa dokar Najeriya da ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Rahotanni sun ce an ɗauki kuɗaɗen ne a wani jirgin helikwafta zuwa sansanin Boko Haram da ke Gwoza a Arewa maso Gabashin Jihar Borno, kusa da iyakar Kamaru, inda aka miƙa su ga Ali Ngulde, wani babban kwamandan ƙungiyar a yankin.
Saboda rashin hanyoyi a cikin dajin, majiyoyin sun ce sai da Ngulde ya tsallaka zuwa ƙasar Kamaru domin tabbatar da isowar kuɗin kafin a saki rukuni na farko na yara 100.
Sai dai Gwamnatin Najeriya ta musanta biyan ko sisi ga ƙungiyar da ta sace kusan ɗalibai da ma’aikata 300 daga makarantar St. Mary’s da ke yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja a ranar 21 ga Nuwamba, inda wasu ɗalibai kusan 50 sun samu damar tserewa daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Sai dai majiyoyi huɗu da suka san yadda tattaunawar ta gudana sun shaida wa AFP cewa an biya “kuɗin fansa masu yawa” bayan wata tattaunawa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranta.
Wata majiya ta ce an biya naira miliyan 40 kan kowane mutum ɗaya, kwatankwacin dala miliyan bakwai gaba ɗaya, yayin da wata ta ce adadin ya kai naira biliyan biyu.
Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS) ta musanta biyan kuɗin, tana cewa: “Jami’an gwamnati ba sa biyan kuɗin fansa,”sai dai ta ƙara da cewa idan iyalai ne suka biya don ceto ‘yan uwansu, babu wanda zai hana su.
Rahoton ya ce an danganta satar da wani fitaccen kwamandan Boko Haram mai suna Sadiku, wanda ake zargi shi ne ya jagoranci harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a 2022, wanda aka karɓi kuɗaɗen fansa masu yawa daga fasinjoji.
Masana sun ce lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsin lamba daga ƙasashen waje, musamman bayan zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa ana tsananta wa Kiristoci a ƙasar.
Duk da dokar da ta haramta biyan kuɗin fansa tun 2022, satar mutane na ci gaba da yawaita a Najeriya, inda rahotanni suka nuna cewa an samu sace-sace 828 a bara kaɗai, kuma galibi sukan shafi mutane da dama a lokaci guda.
Masana sun bayyana matsalar a matsayin “kasuwancin sace-sace” da ta zama hanyar samun kuɗi, wadda ƙungiyoyin masu riƙe da makami da ‘yan fashi ke amfani da ita wajen tara kuɗi masu yawan gaske kuma a cikin ƙanƙanin lokaci a ƙasar da talauci ke ci gaba da addabar jama’a da dama.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link