Ƙungiyar JUSUN Ta Janye Yajin Aiki Bayan Sulhu Da Gwamnatin Kaduna
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kaduna ta warware rikicin da ya shiga tsakaninta da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Nijeriya (JUSUN), reshen Jihar Kaduna, lamarin da ya ba da damar dakatar da yajin aikin mako guda tare da cikakken komawar ayyukan kotuna a fadin jihar.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa gwamnati ta gana da Kwamitin Zartarwa na JUSUN a ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026, a ofishin Babban Lauyan Jihar domin tattauna batutuwan da suka haddasa sabanin.
- Darussa Daga Ramadan Na 5: Tsare Gaɓɓai Daga Saɓo
- Atiku Abubakar Ya Zargi Bola Tinubu Da Raunana Dimokuraɗiyya
Daga cikin bukatun kungiyar akwai aiwatar da cikakken ‘yancin cin gashin kai na bangaren Shari’a ta fuskar kudi, daidaita albashi bisa sabon mafi karancin albashi, biyan bashin albashin watannin Afrilu da Mayu na shekarar 2021, da kuma biyan bashin kudin hutun ma’aikata.
Bayan tattaunawa, an cimma matsaya tare da warware dukkan batutuwan cikin lumana bisa umarnin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Dakta James Kanyip, ya bayyana sakamakon taron yan nuna jajircewar Gwamnan wajen tabbatar da zaman lafiya a ma’aikata da kuma kara inganta ayyukan gwamnati.
Gwamnatin Jihar ta yaba wa shugabannin JUSUN bisa nuna dattako da hadin kai, tare da kira ga dukkan ma’aikatan bangaren shari’a da su koma bakin aiki nan take domin tabbatar da ingantacciyar gudanar da adalci a Jihar Kaduna.
[ad_2]
Source link