An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi
[ad_1]
’Yan sanda sun samu nasarar kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato bindigar AK-47 bayan musayar wuta da su a yankin Shanga na Jihar Kebbi.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru, DPO na Shanga ya gaggauta haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar, inda aka kashe uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.
Kakakin ’yan sandan ya ce wannan nasara na da nasaba da bayanan sirrin da suka tattara cewa wata tawagar masu garkuwa da mutane ta ɓulla a dajin da ke kan hanyar Tungargiwa zuwa Saminaka, suna shirin yin garkuwa da matafiya.
A wani lamari daban, sanarwar ta ce wasu gungun masu garkuwa ɗauke da makamai masu haɗari sun afka garin Kesan a Ƙaramar Hukumar Shanga, inda suka yi garkuwa da wani matashi mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu, mai shekaru 25.
Shi ma dai bayan samun rahoton ne, DPO na yankin ya tura tawagar jami’an tsaro wadda ta bi sawun masu garkuwan har suka ceto matashin da aka sace.
Sai dai yayin aikin ceton, an harbi matashin a ƙafarsa ta hagu, inda yanzu haka yana samun kulawa a wani asibiti da ke yankin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link