Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato

[ad_1]



Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda abin ya rutsa da su sun gaggauta shiga kwale-kwalen ne a ƙoƙarin tsere wa ‘yan bindigar da suka hango sun yi kwanton ɓauna.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Saboda fargaba, mutane da yawa ba sa kwana a gidajensu. Sukan kwana a daji, sai safe su dawo gida. To, a ranar da abin ya faru, suna dawowa ne kwale-kwalen ya kife.”

Kazalika, wani mazaunin ya ce an shiga zaman ɗar-ɗar ne lokacin da suka hangi ‘yan bindigar na tunkaro su, lamarin da ya sa suka yi gaggawar shiga kwale-kwalen da ta kife a tsakiyar ruwa saboda an yi masa lodin da ya fi ƙarfinsa.

Ɗan majalisar dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rashin tsaro ya tilasta mazauna da dama barin gidajensu suna kwana a jeji.

Ita ma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) ta tabbatar da faruwar hatsarin, wadda ta ce jami’inta sun ceto mutum 19 daga cikin ruwa, yayin da ake ci gaba da neman ragowar wasu mutum uku waɗanda suka ɓace.

Wannan mummunan lamari ya sake jaddada tsananin da mazauna Sakkwato ke ciki, inda wasu ƙauyuka suka zama kufai, yayin da ‘yan gudun hijira ke ƙaruwa sakamakon hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *