Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe
[ad_1]
Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira.
Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar.
Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo.
Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin damuwa da alhini.
Kasuwar Katako na daga cikin manyan cibiyoyin hada-hadar kasuwanci a jihar wacce jigo ce wajen samar wa dubban mazauna Gombe kudaden shiga.
Jami’an hukumar kashe gobara sun shiga aikin ceto da wuri domin dakile bazuwar wutar, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a tantance adadin shagunan da suka ƙone ko jimillar asarar da aka yi ba.
Muna tafe da karin bayani…
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link