An fara binciken gawar wani matashi da aka gani rataye a Kano

[ad_1]



Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ta fara gudanar da bincike kan zargin yadda wani matashi mai suna Mubarak Hamisu mai shekaru 28, ya kashe kansa a unguwar Gyadi-Gyadi da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce mazauna unguwar ne suka kai wa ’yan sanda rahoton ganin gawar matashin da misalin ƙarfe 6:10 na safe.

“An tura jami’a zuwa wajen nan take, inda aka samu matashin wanda ake zargin kisan kai ne,” in ji Kiyawa.

Ya ƙara da cewa ba a ga wata alama da ke nuna am cutar da shi ba.

“An kai marigayin Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa,” in ji shi.

An miƙa gawar matashin ga iyayensa domin binne shi bisa tsarin addinin Musulunci.

Ɗan uwan marigayin, Muhammad Ghali Abdulwahab, ya ce: “Mun tashi da wannan abu mara daɗi. An kira ni aka sanar da ni cewa an ga Kurma ya rataye kansa.

“Nan na je wajen. Mun kai shi asibiti inda suka tabbatar da rasuwarsa.

“Ba za mu iya cewa ga abin da ya faru ba, amma ba mu yadda cewa ya kashe kansa ya yi ba.

“An ga wani yanka a wuyansa, hakan alama ce da ke nuna an yi yunƙurin cutar da shi.

“Babu wanda muka zarga a yanzu, amma hukumomin tsaro suna bincike don gano gaskiyar lamarin,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *