Kwamishinan Ilimi Na Zamfara Madawaki Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa
Kwamishinan Ilimi na Jihar Zamfara, Malam Wadatau Madawaki, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Ya ce ya yanke shawarar ne saboda Gwamna Dauda Lawal na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
- EFCC Ta Sanya Alama Kan Kadarorin Malami Da Ake Bincika
- Eid-el-Fitr:Kwankwaso Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Ci Gaba Da Jajircewa Kan Kyawawan Manufa
Madawaki ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa a PDP kuma ba shi da niyyar komawa APC.
Ya kuma jaddada cewa babu wanda ya tilasta masa yin murabus, yana mai cewa shawara ce ta ƙashin kansa.
Gwamnan ya amince da murabus ɗinsa, sannan ya umarci Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Abdulmalik Gajam, ya riƙa kula da ma’aikatar ilimi na wucin gadi.
Gwamnan ya gode wa Madawaki kan ayyukan da ya yi tare da yi masa fatan alheri.
A baya-bayan nan, gwamnan ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC bayan tuntuɓar shugabanni da masu ruwa da tsaki a jihar.