Jirgin soji marar matuƙi ya yi hatsari a Neja
[ad_1]
Jirgin sama marar matuki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya fadi a dajin Zangata da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora, Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da yamma, ƙasa da sa’o’i 48 bayan ’an ta’adda sun kai hari a ƙauyukan Goro da Gebe da ke karamar hukumar Agwara, inda suka kashe manoma biyu tare da ƙona aƙalla gidaje 13.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa waɗannan ƙauyuka na kan iyaka tsakanin Borgu da Agwara, kuma maharan suna gudo ne daga Jihar Kwara bayan hare-haren sojoji a kansu.
Wani mazaunin Kontagora, Zakari Adamu Kontagora, ya ce sojoji da ’yan sanda sun isa wurin, amma ba a tabbatar da irin lalacewar da jirgin ya yi, ko ko akwai asarar rayuka ba.
Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da hatsarin, inda ta ce jirgin ya rasa sadarwa ne da cibiyar bayan an tura shi domin ci gaba da yaƙi da ta’addanci a Neja.
Sanarwar da kakakin rundunar, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya fitar, ya fitar ta ce babu asarar rayuka, kuma ayyukan tsaro a dukkan fagen yaƙi suna ci gaba ba tare da tangarɗa ba.
Ejodame ya ce: “An aiwatar da matakan gaggawa na dawo da jirgin gida. NAF ta kuma hanzarta haɗin gwiwa da sauran rundunoni da hukumomi wajen tsare da ceto na gaggawa.”
Ya ƙara da cewa an riga an gano jirgin, kuma injiniyoyi sun fara tantancewa da aikin dawo da shi bisa ƙa’idojin tsaro da aiki.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link