Samson Adamu Na Nijeriya Ya Zama Sabon Sakatare Janar Na CAF
Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta naɗa Samson Adamu a matsayin sabon Sakatare Janar na hukumar, inda hakan ya sa ya zama ɗan Nijeriya na farko da ya taɓa rike wannan muƙami tun bayan kafuwar CAF kimanin shekaru 70 da suka gabata.
Adamu ya maye gurbin Veron Mosengo-Omba ɗan asalin ƙasar Switzerland, wanda ya ajiye aikinsa kafin wannan naɗin, inda kafin yanzu Samson Adamu ke aiki a matsayin Daraktan Wasanni da Shirye-shirye a hukumar ta CAF.
- Neymar Ya Fi Messi, Ronaldo Da Mbappe Hazaka A Kwallon Kafa – Cafu
- EFCC Ta Cafke Mutane 20 A Zaɓen FCT, Ta Kwato Sama Da Miliyan 17 Wajen Masu Sayen Ƙuri’a
A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF), Dr. Ademola Olajire, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa Kwamitin Zartarwa na CAF ne ya gabatar da sunansa domin maye gurbin Veron.
Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani Majalisar CAF ta amince da naɗin nasa a taronta da aka gudanar ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, 2026, a Otal din Giza Palace da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar.
Naɗin Adamu na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran ƙarfafa tsarin gudanarwa da shirye-shiryen wasanni a nahiyar, tare da ƙara inganta rawar da Nijeriya ke takawa a harkokin ƙwallon ƙafa a matakin Afirka.