Rahoton Jamus: Fasahohin Masana’antu Na Kasar Sin Suna Kan Gaba A Duniya

[ad_1]

Wani rahoto game da ci gaban fasahohin masana’antu a duniya, da jami’ar Munich ta kasar Jamus, da kamfani mai samar da shawarwari na MHP na kasar suka gabatar a kwanan baya, ya nuna cewa, fasahohin masana’antu na kasar Sin suna kan gaba a duniya, musamman ma a fannonin kirkirarriyar basira ta AI, da fasahar sanya na’urorin sarrafa kansu, da dai makamantansu.

A cewar wannan rahoton bincike, ana ganin alamar karuwar yadda ake amfani da fasahohin zamani na dijital a bangaren sana’ar hada kayayyaki a duniya, inda ma’aunin amfani da fasahar dijital a kasar Sin ya kai kashi 72%, wanda ya karu da kashi 3% idan an kwatanta da jimillar ta shekarar 2025. Yayin da jimillar na kasar Amurka a wannan fannin kuwa ita ce kashi 69%.

Masana da suka gabatar da rahoton binciken sun yi nazari kan ra’ayoyi da wakilan kamfanonin masana’antu fiye da 1200 na kasashe daban daban suka bayyana, kafin su sanar da sakamakon bincikensu. Kana galibin wakilan kamfanoni da suka gabatar da ra’ayoyinsu suna aiki ne a sana’o’in da suka hada da aikin samar da injuna da na’urorin zamani, da bangaren sadarwa, da na kera motoci, da dai sauransu. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *