Tarihi Ba Zai Manta Yadda Amurka Ke Zubar Da Jini Da Murƙushe Haƙƙin Ƙasashen Latin Amurka Ba
[ad_1]
Hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela ba wani abu ba ne mai ban mamaki: wannan dai shi ne na kwanan nan a irin al’adarta da ta saba na ayyukan soji domin wargazawa da sauya tsarin gwamnati a duk faɗin Latin Amurka. Daga Guatemala a 1954 zuwa Panama a 1989 da kuma yanzu a Venezuela a 2026, Washington ta yi ta sadaukar da rayuka da ikon gwamnatocin Latin Amurka akai-akai da sunan wai samar da zaman lafiya da kafa dimokuradiyya.
Abin da ya faru a Caracas a 3 ga Janairu abin takaici ne, amma ba abu ne na farko ba, da ma ya riga ya zama al’adar Amurka, gano gwamanti mai fama da ‘yar karamar matsala a cikin gida ko ta shirya manakisar haifar da matsalar, sannan ta fara yi wa kasar barazana, daga nan kuma ta yanke shawarar kashin kanta na amfani da soji wurin sauya gwamnatin.
Amurka ta fara aiwatar da wannan tsarin ne a lokacin da ta hambarar da gwamnatin zababben shugaban Guatemala, Jacobo Arbenz a 1954. Laifinsa ba ta’addanci ko tauye hakkin mutanensa ba ne, kawai ya kawo gyare-gyare ne da za su samar wa kasarsa ‘yancin tattalin arzikinta, ya kalubalanci tsarin tsoma bakin Amurka a harkokin siyasar kasar, wanda hakan zai iya katse abin da Amurka take samu a kasar. Sakon a fili yake, duk kasar da ta nemi ballewa daga bukatun tattalin arzikin Amurka, to gwamnatinta ba za ta tsira ba.
Kifar da gwamantin Arbenz da tallafin CIA ya haifar da mika kasar zuwa ga jerin gwamnatocin soji wadanda suka taimaka wajen jefa ƙasar cikin yakin basasa na shekaru 36, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200,000 galibi ‘yan asalin kasar.
A Chile, matsin lamba na Amurka da kuma kulla manakisa sun taimaka wajen wargaza zababbiyar gwamnatin Salvador Allende sannan kuma sun share fagen juyin mulkin Augusto Pinochet na 1973. Wannan manakisar, ta haifar da mutuwar dubban mutane ko tarwatsa su, sannan ya jefa kasar cikin mummunan yanayin tattalin arziki.
A Nicaragua, lokacin da kungiyar ‘yantar da jama’a ta Sandinista National Liberation Front ta kifar da mulkin kama-karya mai goyon bayan Amurka, Washington ta fara tallafawa sojoji masu adawa da gwamnati a kasar da kudade, ba wai kawai horar da ‘yan adawan ta yi ba, har ma da ƙarfafa su wajen sanya nakiyoyin ruwa a manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar. Yakin basasa da Amurka ta haifar ya jefa kasar cikin rikice-rikice, da yawaitar makamai a hannun wadanda ba su cancanta ba na tsawon lokaci. Saboda fama da rikice-rikice na tsawon lokaci, ya mayar da kasar a matsayin daya daga cikin kasashe mafi talauci a Yammacin Duniya.
A Panama, a kokarin Amurka na samun karfin iko na dindindin a mashigin ruwan Panama, ta tura manyan dakarun sojinta a shekarar 1989 don kifar da gwamnatin sojin kasar, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar kusan ‘yan Panama 500.
Tarihi na nan kuma ba ya tafiya, duk wadannan kasashen da muka ambato muku, Amurka ta yi musu kutse ne da ikirarin samar da ‘yanci, wanzar da zaman lafiya ko kafa dimokuradiyya, amma wacce kasa ce Amurka ta kutsa sannan ta fita ta bar ta da alheri? Sai dai wargazawa, ruguzawa da tarwatsa tattalin arzikin kasar.
Haka in muka duba abin da ya faru kwanan nan a Venezuela, ya yi daidai da irin tsarin da Amurka ta aiwatar a kasashen da muka ambato a baya. Ta tura jiragen sama na yaki masu saukar angulu da dama cikin kasar a tsakar dare, ta kaddamar da hare-hare a Caracas, da kuma kama Shugaban kasa mai ‘yanci, Nicolas Maduro, duk akan wannan ikirarin nata da ta saba, wai samar da zaman lafiya da bayar da tsaro a yankin Latin Amurka. Amma duniya ta san ainihin manufar Amurka.
Abu mafi muni da aka fi tsoro, mummunan tarihin irin abun da ya faru da Guatemala, da Chile, da Nicaragua, zuwa Panama, wanda ya nuna karfin bindigar Amurka baya haifar da dimokuradiyyar da take ikirari face haifar da rikice-rikice da tabarbarewar tattalin arzikin kasa.
Yankin Latin Amurka, ba dajin Allah ba ne zalla da babu mai shi, ballantana Amurka ta ce, za ta sarrafa tsarin jagorantar shi yadda take so. Yanki ne mai tarihi, da cibiyoyi, da yake da burikan shi. Kasashen da suka sha wahalar juyin mulki da danniyar Amurka a karni na 20, tarihin Guatemala 1954, da Chile 1973, Nicaragua a 1980, da Panama 1989, yanzu shi zai haskaka musu hanyar ganin wannan sabon harin da aka kai wa Caracas a shekarar 2026.
Duk wani shiri da Amurka za ta aiwatar, babu abin da zai haifar, face maimaita tarihin abin da ta taba yi a yankin. Don haka, ba laifi ba ne, in an ce, Amurka ba ta ganin yankin a matsayin makwabciya sai dai kawai kamar wani yankin bayinta ko kuma filin gwada karfin sojinta.
[ad_2]
Source link