Kakakin Sin: Sin Da Afirka Sun Zama Abin Koyi Na Sabon Salon Dangantakar Kasa Da Kasa


Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai soma ziyararsa a wasu kasashen Afirka a wannan makon, shekaru 36 ke nan a jere da ministocin harkokin wajen kasar Sin ke yin ziyararsu ta farko a kasashen waje a yankin Afirka. Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis cewa, Sin da Afirka sun kasance abin koyi na sabon salon dangantakar kasa da kasa, wadanda kuma suke kan gaba wajen inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adam.

Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin na son yin aiki tare da bangarori daban daban don kara ba da gudummowa kan inganta zaman lafiya da zaman karko da kuma ci gaban nahiyar Afirka bisa ga tushen girmama ikon mulkin kanta. (Bilkisu Xin)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *