Yadda jama’a suka yi cikar ƙwari a Maulidin Inyass karo na 40 a Katsina
[ad_1]
Dandazon jama’a sun yi cikar ƙwari domin gudanar da bikin Mauludin fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Inyass, karo na 40 a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke kan hanyar Mani a Jihar Katsina.
Taron maulidin ya gudana ne a ranar Asabar 17 ga watan Janairu, 2025.
Taron ya samu halartar manyan malamai da mabiyansu daga sassa daban-daban na Najeriya da kuma wasu ƙasashe.
Wasu daga cikin mahalarta sun isa Katsina tun kwanaki biyu kafin ranar taron.
An fara gudanar da mauludin Inyass a garin Kaulaha na ƙasar Senegal a shekarar 1986, bayan shekaru 11 da rasuwar malamin.
An haifi Sheikh Ibrahim Inyass a shekarar 1900 a Kaulaha, ya rayu tsawon shekaru 75.
A tsawon rayuwarsa, ya yi karatun addini tare da yaɗa ilimin addinin Musulunci zuwa ƙasashe da dama na Afirka, ciki har da Najeriya, kuma ya rasu a shekarar 1975.
Daga cikin manyan baƙi akwai shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya na Afirka, kuma Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, wanda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya tarbe shi.
A jawabin da ya gabatar, Gwamna Radda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa rayuwar al’umma tare da goyon bayan harkokin addini.
Haka kuma, ya yi magana kan inganta zaman lafiya a jihar, inda ya ce tsaro ya samu ci gaba sosai.
An gudanar da mauludin cikin kwanciyar hankali tare da tsaurara matakan tsaro.
Haka kuma, taron ya kawo bunƙasar tattalin arziƙi, inda ƙananan ’yan kasuwa kamar masu sayar da abinci, wanzamai, masu babura da masu hayar ɗakuna suka yi hada-hada sosai.
Ga hotunan yadda maulidin ya gudana:
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link