Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis
[ad_1]
Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a ranar Alhamis, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Bullah Audu Bi-Allah ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
A makon da ya gabata ne, Shugaba Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Amupitam, domin ta tabbatar da naɗinsa.
An karanta wasiƙar Tinubu yayin zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
A cikin wasiƙar da ya aike, Tinubu, ya ce: “Dangane da sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), ina farin cikin gabatar da Farfesa Joash Amupitan (SAN), domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
“Na haɗa da taƙaitaccen tarihin aikinsa, kuma ina fatan Majalisar Dattawa za ta duba kuma ta tabbatar da naɗinsa cikin gaggawa.”
Sanarwar da Ofishin Yaɗa Labarai na Majalisar, ya fitar ta kuma bayyana cewa za a tantance shi a a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoba, 2025.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link