Kwamishina ya yi murabus saboda takarar shugabancin APC a Kano

[ad_1]



Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Umar Haruna Doguwa, yayin da ake hasashen zai tsaya takarar shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce Doguwa ya miƙa takardar murabus ɗinsa tun a ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026.

Gwamna Yusuf ya yaba masa bisa jajircewa da hidimata wa al’ummar Kano, yana mai jinjina da irin rawar da ya taka a Ma’aikatar Ilimi kafin daga bisani a mayar da shi Albarkatun Ruwa, inda aka samu ci gaba wajen gyaran rumbunan ruwa da faɗaɗa samar da ruwan sha a sassan jihar.

Sai dai majiyoyi sun ce murabus ɗin na da alaƙa da shirin Doguwa na tsayawa takarar shugabancin APC a Kano gabanin babban taron jam’iyyar da za a yi a Dandalin Wasanni na Kofar Mata.

Jam’iyyar ta ce ta kafa kwamitoci uku domin tabbatar da sahihanci da zaman lafiya a taron, tana mai jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin gida da haɗin kai a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *