Da Pan Ji: Abincin Sinawa Da Na Fi So
[ad_1]
Da farko mai karatu ka sani, ba fa santi nake ba, ko da yake idan ma na yi santi ai daidai, domin abu mai bata rai ake boyewa, abin nishadi kuma bayyana shi ake. Sinawa suna da nau’o’in abinci bila’adadin wadanda suka amsa sunansa a matakin kasa da kasa saboda yadda nake ganin baki daban-daban suna ci, sai dai ni, babu wanda ya zama lamba daya a wurina kamar “Da Pan Ji”.
A cikin harshen Sinanci, “Da” na nufin “Babba”, sai “Pan” na nufin “Faranti” ko “Kwano”, sannan “Ji” na nufin “Kaza”. Kila mai karatu ka fahimci sunan abincin yanzu ko? To amma ni na fassara sunan abincin da Hausa na sa masa sunan “Babban Akushin Kaza”.
Ban san yaya ake sarrafa shi ba, ni dai muna haduwa da shi wurin ci. Amma daga abin da na fahimta, “Da Pan Ji” ya kunshi naman kaza da kayan lambu da dankalin turawa ko taliya da kuma kayan kamshi na girki duk a cikin babban faranti, ko babban kwano daya. Ana yin sa da dan romo-romo, kuma naman kazar yana da taushi, ta yadda ko tsoho da yaro za su iya ci ba tare da jin tauri ko tsukawa mai wahalarwa ba.
“Da Pan Ji”, abinci ne wanda yake nuna yadda Sinawa ke son abinci mai cike da hadin kai saboda yadda ake ci tare da iyali ko abokai, kamar yadda yake a bisa al’adarsu ta cin abinci tare don kara kusanci da zumunci a tsakanin jama’a. Hatta ni kaina ba na ci ni kadai sai tare da wani aboki, idan kuma na nemi abokin ci ban samu ba, sai dai na kasa kashi uku, na yi saura da kashi biyu.
Sinawa suna da hanyoyi kala-kala na sarrafa naman kaza ta hanyar dafawa ko gasawa ko soyawa, amma salon “Da Pan Ji”, ni dai a wurina, shi ne ya yi zarra musamman yadda ya kasance “ciki lafiya, baka lafiya”.
Kazalika, bisa yadda ake kawo “Da Pan Ji” cikin kankanen lokaci bayan yin oda a shagon cin abinci, ina tunanin ba shi da wuyar sarrafawa. Don haka nake ganin “Da Pan Ji” yana kunshe da ma’anar da ta zarce abinci kawai, alama ce ta rayuwa mai sauki kuma ina da yakinin duk wanda ya gwada cin sa tare da tafakkuri a kai, zai fahimci cewa wannan abincin na Sinawa ba kawai abinci ba ne, har ila yau darasi ne kan yadda ake tsara rayuwa cikin sauki da zumunci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link