Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Salon Cimma Moriyar Bai Daya Tsakanin Sin Da Faransa
[ad_1]
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin tun daga gobe Laraba 3 zuwa Juma’a 5 ga watan nan, ziyarar da za ta kasance ta hudu da shugaban na Faransa zai gudanar a kasar Sin.
Yayin da ake cikin yanayin cudanyar sassan kasa da kasa mai sarkakiya da tsanani, Sin da Faransa na bukatar nunawa duniya cewa, hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe masu karfin fada-a-ji, ba batu ne na wani ya samu wani ya tafka asara ba, maimakon hakan, suna iya cimma moriyar juna ta hanyar gudanar da shawarwari masu ma’ana.
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta tsara, domin jin mahangar al’ummun kasa da kasa, ya nuna yadda kaso 76.1 bisa dari suka amince cewa, a matsayin muhimman kasashe da suka yi nasara a yayin yakin duniya na biyu, kana masu kujerun dindindin a kwamitin tsaron MDD, ya dace Sin da Faransa su hada hannu wajen kare sakamakon yakin duniya na biyu, da odar kasa da kasa da aka cimma bayan yakin duniyar, tare da jagorantar al’ummun kasa da kasa wajen yin aiki tare, don shawo kan tarin kalubalen dake addabar duniya.
A daya bangaren kuma, kaso 86.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin manufofin Sin na samar da ci gaba mai inganci, da bude kofa bisa babban matsayi, za su samar da sabbin damammakin hadin gwiwa ga Sin da Turai. Yayin da kaso 80.2 bisa dari suka jaddada cewa, gwargwadon kara sarkakiya, da tsanantar yanayin cudanyar kasa da kasa, gwargwadon muhimmancin hadin gwiwa tsakanin Sin da Turai. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link