Sin Ta Gabatar Da Shirin Inganta Lafiyar Yara Da Matasa Na Nan Zuwa Shekarar 2030
[ad_1]
A yau Talata ne kasar Sin ta gabatar da shirin inganta lafiyar yara, da matasa masu karancin shekaru, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2026 dake tafe zuwa 2030, inda aka tsara tunkarar matsalolin kiba fiye da kima, da karancin gani daga nesa, da ciwon kwakwalwa da na dabi’u, da ciwon dake haifar da tawaya a kashin baya, da lafiyar hakora.
Ana sa ran shirin zai samar da zarafi na kyautata lafiyar jikin matasa, da inganta lafiyar tunaninsu ta hanyar karfafa kandagarki, da tsare-tsaren jagorancin magance larurorin lafiya masu tarin yawa.
Har ila yau, shirin ya bukaci kara azamar karfafa hadin gwiwa tsakanin hidimomin kiwon lafiya da makarantu, da dunkule sassan kula da lafiya da na ilimin motsa jiki, da inganta hadin kai tsakanin makarantu da iyalai, da karfafa gwiwa wajen shigar al’umma cikin ayyukan bunkasa lafiyar matasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link