Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil.
Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Manyan jami’an gwamnati da suka raka shi, sun haɗa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; da Ministan Kuɗi, Wale Edun.
A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci Taron Ci Gaban Afirka karo na tara (TICAD9) wanda zai gudana a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Taken taron shi ne “Haɗa Hannu Wajen Samar da Ingantacciyar Mafita ga Afirka”.
Taron zai mayar da hankali kan inganta tattalin arziƙin Afirka, kyautata yanayin kasuwanci, da samar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaba mai ɗorewa ta hanyar jari-hujja da ƙirƙire-ƙirƙire daga kamfanoni masu zaman kansu.
Bayan taron Japan, Tinubu zai nufi ƙasar Brazil, domin ziyarar aiki ta kwana biyu daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Agusta.
Tinubu zai je ƙasar ne bayan gayyatar da Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya yi masa.
A Brazil, zai gana da shugaban ƙasar, sannan zai halarci taron kasuwanci, kuma ya tattauna hanyoyin bunƙasa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Tawagarsa za ta kuma yi aiki wajen ƙulla yarjejeniyoyi da haɗin gwiwa da gwamnatin Brazil.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link