An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato
[ad_1]
Rundunar ’yansandan Jihar Sakkwato ta kama wani mai shekaru 25 a duniya, Sufiyanu Aliyu, daga ƙauyen Gwanyal a ƙaramar hukumar Tangaza, bisa zargin kashe matarsa mai shekaru 15, Suwaiba Abubakar Bawa.
’Yansanda sun ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoba, 2025, bayan rikici ya ɓarke tsakanin ma’auratan.
Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 8 na dare, inda jami’ai suka garzaya wajen da abin ya faru.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya soki matarsa da wuƙa yayin da suke faɗa.
’Yansanda sun samo wuƙar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen kisan, sannan suka kai gawar mamaciyar asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.
Rufai, ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, kuma an gurfanar da shi a kotu, yayin da aka miƙa shi sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin ƙara bincike.
Kwamishinan ’yansanda na jihar ya yaba wa jami’ansa bisa yadda suka hanzarta kai ɗauki, tare da tabbatar wa da jama’a cewa za a tabbatar da adalci a cikin lamarin.
[ad_2]
Source link