Ɗalibai 2 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Borno
Wasu ɗalibai biyu sun rasu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a yankin Baga, da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Ɗaliban sun haɗa da Musa Abdulhadi, daga makarantar sakandaren gwamnati ta GDSS Baga, da kuma wata ɗaliba daga Kwalejin Addinin Musulunci ta Baga, wadda ba a bayyana sunanta ba.
Shugaban makarantar GDSS Baga, Lawan Gare Baga ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar 16 ga watan Disamba, 2025.
Ya ce an yi ƙoƙarin ceto ɗaliban na tsawon kwanaki biyu, amma abin ya ci tura.
A cewar makarantar, kwale-kwalen da ɗaliban ke ciki ne ya kife a ruwa, lamarin da yayi sanadin rasuwarsu.
Shugaban makarantar ya ce Musa Abdulhadi ɗalibi ne mai halin kirki, biyayya da ladabi.
Ya ƙara da cewa an ga mamacin cikin koshin lafiya da farin ciki a lokacin taron rufe makaranta a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Ita ma ɗalibar da ta rasu an bayyana ta a matsayin yarinya mai hazaƙa da biyayya.
Makarantar ta bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansu, ya kuma bai wa iyayensu haƙurin jure wannan babban rashi.