Sin Ba Ta Neman Fifiko Ta Hanyar Rage Darajar Kudinta In Ji Gwamnan Babban Bankin Kasar

[ad_1]

Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce Sin ba ta bukata, kuma ba ta da niyyar samun wani fifikon cinikayyar waje, ta hanyar rage darajar kudinta.

Pan Gongsheng, ya bayyana hakan ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai, a gefen taro na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14. Ya ce har kullum babban bankin kasar Sin PBOC, na taka rawar gani wajen daidaita yanayin kasuwa ta fannin tsara kimar musayar kudi, da wanzar da sassauyawar darajar musaya, da karfafa hasashen ayyukan gudanarwa, da wanzar da darajar musayar kudin kasar wato yuan kan madaidaicin mizani, bisa managarcin yanayi.

Gwamnan babban bankin na Sin, ya ce a gabar da kamfanoni daban daban ke kara amfani da musayar kudi, ko biyan kudaden cinikayya tsakanin kasashe daban daban da kudin Sin yuan, sama da kaso 60 bisa dari na hada-hadar shige da ficen hajojin Sin, na gudana bisa kariya daga mummunan tasirin sauyin kimar kudaden musaya, adadin da ake hasashen zai karu nan gaba cikin shekarar nan ta bana. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *