An kama mai shekaru 74 da hodar iblis a filin jirgin saman Abuja

[ad_1]



Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), sun kama wani mutum mai shekaru 74 a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bisa zargin yunƙurin safarar hodar iblis.

An kama mutumin, mai suna Ikwuakalom Nwakoro Emeka ne, a ranar Asabar yayin da ake binciken fasinjoji kafin hawa jirgin kamfanin British Airways da yake shirin zuwa Landan.

Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa mutumin ya yi iƙirarin cewa zai tafi Landan ne domin yin hutu.

Sai dai yayin binciken kayayyakinsa, jami’ai sun gano hodar iblis da aka ɓoye a cikin kayan abinci.

Hukumar ta ce nauyin ƙwayar ya kai kilo 11, kuma an ɓoye ta ne a cikin niƙaƙƙen busasshen barkono, sannan aka naɗe ta da takarda.

Babafemi ya ƙara da cewa wannan kamun na daga cikin jerin samamen da NDLEA ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan domin daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi.

A wani samame na daban kuma a birnin Legas, jami’an NDLEA sun kama wata mata mai suna Maryam Olalowo a wani otal da ke Victoria Island, inda ake zarginta da yunƙurin sayar da giram 89 na hodar iblis da giram 20 na wiwi.

An kama ta ne tare da ‘ya’yanta guda uku, har da jiri.

Yayin da ake yi mata tambayoyi, ta shaida cewa ƙwayoyin na mijinta ne, Ibrahim Olatunji.

Daga bisani, jami’an NDLEA sun yi nasarar kama Olatunji bisani.

Hukumar ta bayyana cewa ya amsa laifinsa na mallakar ƙwayoyin, sannan bincike ya nuna cewa an taɓa kama shi a shekarar 2015 inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi kan irin wannan laifi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *