Xi Ya Halarci Taron Sabuwar Shekarar Sinawa Tare Da ‘Yan Siyasar Da Ba JKS Ba
[ad_1]
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya mika gaisuwar murnar bikin sabuwar shekara ga ‘yan siyasar da suka fito daga sauran jam’iyyun siyasa da ba JKS ba, da kuma kungiyar masana’antu da kasuwanci ta kasar Sin baki daya, da wadanda ba su cikin kowace jam’iyyar siyasa, da sauran mambobin gamayyar kare muradun kasa, gabanin zuwan bikin bazara, ko kuma sabuwar shekara ta gargajiyar Sinawa.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin tsakiya na soja, ya mika sakon gaisuwar ne yayin da yake halartar taron shekara-shekara tare da ‘yan siyasar da ba mabiya jam’iyyar JKS ba, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link