Yadda na tsira a hatsarin jirgin ruwan Goronyo — Hakimi
[ad_1]
Ɗaya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin ruwa a yankin Kojiyo da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato ya shaida wa Aminiya ainihin yadda abin ya faru.
A ranar Lahadin da ta gabata ne jirgin ruwa ya kife da mutane sama da 30, yawancinsu ’yan kasuwa ne a hanyarsu ta komawa gida bayan cin kasuwar garin Goronyo.
Hakimin garin, Alhaji Nasiru Magajin Kojiyo, wanda ya tsallake rijiya da baya a hatsarin ruwan, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Bayan jirgin ya kife, waɗanda ke iya fito suka fita cikin ikon Allah, waɗanda suka kasa ruwan ya tafi da su.
“A lokacin kowa ta kansa yake yi, amma mu da muka tsira za mu kai mutum shida zuwa bakwai,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin Kojiyo, Nasiru Goronyo, ya shaida wa Aminiya cewa jirgin, “A yanzu mutane 30 da jirgin ya ɗauko babu wanda aka fitar da shi a ruwan, sai dai an samu fitar da babur ɗaya daga cikin takwas da suka nutse.”
Amma Shugaban Ƙaramar Hukumar Goronyo, Zubairu Yari, ya ce an ceto aƙalla mutum huɗu.
“’Yan kasuwar sun zo ne daga wurare daban-daban har da Gada don cin wannan kasuwar. Ana kan ƙoƙarin ceto mutanen, ruwa sun yi yawa domin dam na Goronyo ya zubo ruwa. Gudun kar ya yi ambaliya aka buɗe shi.”
Ya yi kira ga maƙwabtan garuruwa da su taimaka su kawo gawar waɗanda ruwan ya cinye idan sun gani, yana da tabbacin za a samu ganin wasu da suka ɓata.
Shugaban ƙaramar hukumar ya danganta lamarin da ɗaukar lodi fiye da kima a kan jiragen ruwa da kuma rashin hanyar mota mai kyau da ya sa yawancin mutane yin sufurin ruwa.
Ya ce duk da haka a yanzu gwamnati na gina hanyoyi da gadoji a yankin kuma an hana jiragen ruwa ɗaukar kayan da suka fi ƙarfin su tashi.
Amma Alhaji Nasiru, wanda ya tsallake rijiya da baya a hatsarin, ya danganta hatsarin da rashin ingancin jirgin. Ya ce jirgin na katako ne kuma ya nutse ne bayan shigar ruwa cikinsa:
“Sun yi yawa an kasa shawo kai, amma ba an ɗaura masa kaya ne da suka wuce kimarsa ba.”
Babban Jami’in Kula da Ayyuka na Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Aliyu Shehu, ya bayyana cewa jirgin ruwan ya ɗauko mutane 51 tare da kayansu da babura kafin ya tuntsure.
“Ƙoƙarin ceto mutanen na tafiya kuma mun sanar da garuruwa maƙwabta su taimaka wajen bincikar mutanen a wurin da suke,” in ji shi.
A lokacin da manema labarai suka tafi wurin dangin waɗanda suka nutse, sun yi jungum saboda rashin tabbas game da ’yan uwansu.
Jami’ai daga Hukumar Kula da Gulabe ta Ƙasa (NIWA) sun tafi wurin, inda Manajan Yanki, Injiniya Muhammad Bala, ya nuna rashin jin daɗin hukumar kan hatsarin. Ya yi kira ga matukan jirgi su rika kula da ka’idar tuki, su daina ɗaukar fasinja da yawan da ya wuce kima.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da tallafin Naira miliyan 20 da buhuna 100 na kayan abinci ga iyalan waɗanda abin ya shafa. Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Idris Muhammad Gobir, yayin ziyarar jajensa ya tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na tallafa wa iyalan da abin ya shafa tare da aiki tare da hukumomi domin ƙarfafa matakan tsaro a kan hanyoyin ruwa a fadin jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link