Sheikh Joaan Ya Zama Sabon Shugaban Kwamitin Olympics Na Yankin Asiya
An zabi Sheikh Joaan Bin Hamad Al Thani na kasar Qatar a matsayin sabon shugaban kwamitin majalisar wasannin Olympics na Asiya (OCA), an gudanar da zaben ne a ranar Litinin a babban taron OCA na 46 da aka gudanar a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan, wakilai 45 daga kwamitin Olympics na Asiya (NOCs) ne suka halarci taron, tare da Shugaban Jamhuriyar Uzbekistan, H.E. Shavkat Mirziyoyev.
Sheikh Joaan, wanda ke rike da mukamin babban mataimakin Shugaban gamayyar kwamitocin Olympics na Duniya (ANOC), kuma shugaban kwamitin Olympics na kasar Qatar, ya zama shugaba na 22 da zai jagoranci kwamitin Olympics na Asiya tun lokacin da aka fara wasannin Olympics a shekarar 1913, zai kammala wa’adin tsohon shugaban kwamitin Randhir Singh wanda ya ajiye mukaminsa saboda dalilai na Lafiya.
A jawabinsa na godiya Sheikh Joaan ya bayyana burikansa wajen habaka wannan kwamitin, wadanda suka hada da karfafa hadin kai da ci gaba, tallafawa bangaren wasanni, shugabanci nagari, da kuma mayar da wasanni wata hanya ta samar da fahimta da zaman lafiya a tsakanin kasashen Duniya.