Gwamnatin Sin Ta Aika Da Sakon Taya Murna Ga ‘Yan Wasan Kasar Da Suka Halarci Gasar Paralimpics Karo Na 14

[ad_1]

Kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta Sin, sun aika da sakon taya murna ga tawagar ‘yan wasa masu bukata ta musamman ta Sin da suka halarci gasar wasannin Paralimpics ta lokacin hunturu karo na 14.

Sakon wanda aka aika jiya Lahadi ya bayyana cewa, a gasar wasannin Paralimpics na lokacin hunturu karo na 14 da aka kammala, ‘yan wasa masu bukata ta musamman na Sin sun lashe lambobin yabo 44, ciki har da zinare 15, azurfa 13 da tagulla 16, inda suka zo na farko a yawan lambobin zinare da kuma yawan lambobin yabo gaba daya. Sun samu nasara a fagen wasanni da kuma nuna sadaukarwa, kuma sun samar wa kasar Sin da al’ummarta karin daraja da daukaka a fagen wasanni.

A cikin sakon nasu, kwamitin tsakiyar JKS da majalisar gudanarwa ta Sin sun yaba wa ‘yan wasan masu bukata ta musamman na Sin da suka nuna kyakkyawan hali na jajircewa da dogaro da kai da kuma kyakkyawan fatansu na samun ci gaba a sabon zamani, wanda ya kara ingiza kishin kasa da ruhin gwagwarmaya na ‘yan uwantakar Sin a cikin gida da wajen kasar. Matakin da ya karfafa musu gwiwar kara kokarin hidima ga kasa, da kuma samar da karin nasarorin wasanni.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *